An Kwashe Mutane A Fadar White House Bayan Wani Ya Shigo Ba Izini

  • Lambar Labari†: 638845
  • Taska : http://hausa.irib.ir/
Brief

Jami’an tsaron fadar White House ta shugaban kasar Amurka sun kwashe jami’an fadar da ‘yan jarida da suke ciki da tara su a wani waje mafi aminci na wani lokacin bayan da wani mutum ya tsallake katangar fadar da shigowa cikin fadar da gudun tsiya.

Wani faifan bidiyo ya nuna mutumin da ba a tantance ko waye ba ya tsallako kagantar fadar White House inda ya nufi asalin gidan da shugaban Amurkan Barack Obama yake tare da iyalansa.

 

Rahotanni dai sun ce shugaba Obaman ba ya cikin gidan a lokacin da lamarin ya faru, don kuwa ya riga da ya bar fadar tare da ‘ya’yansa zuwa daya daga wajajen shakatawar shugabannin Amurka na Camp David.

 

Cibiyar tsaron Amurkan da ke da alkalin kare shugaban kasar da sauran manyan jami’ai da iyalansu dai ta yi gum da bakinta kan wannan lamarin wanda ya ke a matsayin babbar barazana ga fadar White House din da ake bayyana ta a matsayin waje mafi tsaro a duniya. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky