An Ja Kunnen Kasar Jordan Kan Hada Kai Da Amurka Wajen Fada Da ISIS

  • Lambar Labari†: 637642
  • Taska : http://hausa.irib.ir/
Brief

Wasu kungiyoyi da jam’iyyun ‘yan adawa a kasar Jordan sun ja kunnen gwamnatin kasar dangane da shiga cikin hadin gwiwan da Amurka take kokarin hadawa wajen yakar kungiyar nan ta Da’ish ko ISIS.

A jiya asabar ne hadin gwiwan jam’iyyun ‘yan gurguzu na kasar Jordan din suka kirayi gwamnatin kasar da ta yi watsi kugen yaki da ‘yan kungiyar Da’ish din da Amurka ta kada, suna masu cewa gwamnatin za ta iya fada da ‘yan kungiyar ta Da’ish mai kafirta musulmi ta hanyoyi daban-daban ba tare da shiga cikin hadin gwiwan Amurkan ba.

 

‘Yan jam’iyyar sun kara da cewa wannan shiri na Amurka wani kokari ne kawai mulkin mallaka a yankin Gabas ta tsakiya da kuma rura wutar yakin kabilanci da ayyukan ta’addanci a yankin.

 

Jami’ai da ‘yan siyasar kasashe daban-daban na yankin Gabas ta tsakiyan da ma wasu kasashen duniya suna ci gaba da sanya shakku cikin aniyar da gwamnatin Obama ta Amurkan ta sanar na fada da ‘yan kungiyar ta ISIS a Iraki da Siriya. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky