An bayyana cewa Amurka tana fakewa da yaki da ta'addanci domin cimma wata manufarta

  • Lambar Labari†: 637430
  • Taska : http://hausa.irib.ir/
Brief

An bayyana sabon yakin da Amurka ta ke son shelantawa a yankin gabas ta tsakiya da sunan fada da ta’addanci a matsayin wani yaudara.

 Wani tsohon jami’in gwamnatin Amurkan ya fadawa tashar telbijin din Presstv cewa; Amurka tana fadin cewa za ta yi yaki da kungiyar Da’ish, ko kuma Isis, sai dai abin tambaya anan shi ne su wanene su ke bai wa kungiyar kudi da makamai? Arthor t. Olive ya ci gaba da cewa; Kungiyar ta Isis, tana gudanar da ayyukanta ne na ta’addanci saboda kudaden da ta ke samu, da kuma za ta daina samun wadannan kudaden to da ta daina  aikin ta’addancin. Olive ya ci gaba da cewa; Abinda Amurkan ta sanya a gaba shi ne kifar da gwamnatin Basshar Assad ta syira da sunan yaki da ayyukan ta’addanci. A jawabin da shugaban kasar Amurka ya gudanar a ranar laraba akan yaki da kungiyar Isis, Barrack Obama ya ce za su yaki kungiyar hatta a cikin Syria, sai dai a lokaci guda ya kore cewa za su yi aiki tare da gwamnatin Syria. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky