Amurka na neman hadin kan kasashen Larabawa a yakin da zata yi da kungiyar IS

  • Lambar Labari†: 637428
  • Taska : http://www.hausa.rfi.fr/
Brief

Yau Asabar Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya isa birnin Alkahiran kasar Masar, don neman goyon bayan wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya, a yakin da Amurkan ke shirin farawa da mayakan kungiyar IS a kasashen Syria da Iraqi.

Ana sa rai Mr. Kerry zai gana da shugaban kasar ta Masar Abdel Fattah al-Sisi, da shugaban kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Nabil al-Arabi. 
Jiya Juma’a shugaban Faransa Francois Hollande ya zama shugaban wata kasa na farko, daya je Iraqi tun bayan da ‘yan tawayen suka karbe wasu sassan kasar a watan Yuni.
A halin da ake ciki, an bayyana Janar John Allen mai ritaya, daya taba jagorantar dakarun kungiyar NATO a Afghanistan, a matsayin wanda zai jagoranci dakarun kasashen duniya da zasu fafata da mayakan na IS. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky