Amurka ta bukaci kafa Dokar hana Turawa taya Larabawa Yaki

  • Lambar Labari†: 636814
  • Taska : http://www.hausa.rfi.fr/
Brief

Kasar Amurka ta bukaci kwamitin tsaro na Majalisar dunkin Duniya da ya samar da wani sabon kudirin Dokar da zai tilastawa kasashen duniya yin Doka a cikin kundin tsarin mulkinsu domin hana kasashen barin al’ummominsu na fita kasashen zuwa wasu kasashen da ake rikici domin shiga cikin kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irinsu ISIS ta kasar Iraki

Kudurin dai ya bukaci gwamnatocin kasashen duniya da su dauki matakan hanawa wasu kasashe daukar mayaka, da kuma hana al’ummominsu fita kasashen da niyar shiga cikin ‘yan ta’adda, ko kuma samun horo kan haka.

Shi dai kudurin, duk da cewa ya yi jam’u ne ga daukacin ‘yan ta’adda a Duniya, babbar manufarsa ita ce kungiyoyin majahidan kasashen larabawa da nahiyar Turai da ke yaki a kasashen Syriya da Iraki, bayan mayakan kungiyoyin majahidan ISIS ko kuma ta al-Nusra.

Kudurin da Amurukar ta bukata dai an makalashi ne a babi na 7 na kundin yarjejeniyar Msajalisar dunkin Duniya, wanda ya tanadi ladabtar da duk wata kasa a Duniya da ta ki yin aiki da dokar da aka tanada. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky