Rikici Tsakanin Obama Da Majalisar Amurka

  • Lambar Labari†: 614955
Brief

Rikici Tsakanin Obama Da Majalisar Amurka Na Ci Gaba Da Kamari

Rahotanni daga Amurka suna nuni da cewa ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin shugaba Barack Obama ta kasar da kuma ‘yan majalisar kasar dangane da musayen fursunoni da gwamnatin ta yi da kungiyar Taliban ba tare da masaniyar majalisar ba.   Lamarin ya sake kamari ne a jiya Litinin bayan da wani jami’in fadar White House din ya gaya wa ‘yan majalisar cewa kimanin jami’ai 90 na gwamnatin suna sane da batun musayen, sai dai kawai ba a sanar da ‘yan majalisar ba ne.   Wannan kalami na jami’in fadar White House din ya fusata ‘yan majalisar inda wani dan majalisar wakilan Amurkan na jam’iyyar Republican Greg Walden ya ce abin bakin ciki ne yadda fadar White House din ta gagara amincewa da koda guda  daga cikin ‘yan majalisar na jam’iyyar Republican ne ko kuma na Democrat mai mulki.   Fadar ta White House dai tana kokari ne wajen kwantar da hankalin ‘yan majalisar wadanda a kwanakin baya wani ya yi barazanar gabatar da kudurin tsige shugaba Obama a majalisar matukar ya sake musayen fursunoni ba tare da ya sanar da ‘yan majalisar ba.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky