Sakin 'yan Taliban ba shi da hadari -obama

  • Lambar Labari†: 612768
Brief

Shugaba Barrack Obama yace gwamnatin Qatar ta ba shi tabbacin cewa tsaron Amurkar ba zai fuskanci barazana ba sakamakon sako manyan mayakan kungiyar Taliban su 5 da aka yi daga sansanin Guantanamo.

An dai yi musayar fursunonin 5 ne da wani Sojan Amurka Sergeant Bow Bergddhl, wanda shi ne soja guda da ya rage a hannun 'yan Taliban fiye da shekaru 4 a Afghanistan.

A wani jawabi da ya yi wa manema labarai a fadar White House, Mr. Obama ya gode wa gwamnatin kasar Qatar din kan shiga tsakanin da ta yi wajen tattaunawa tsakanin Amurka da kungiyar Taliban.

''Mun himmatu wajen ganin mun kawo karshen yakin da ake a Afghanistan kuma mun himmatu wajen ganin mun rufe sansanin Guantanamo. Mun lashi takobin ganin mun dawo da fursunoninmu na yaki gida'' inji shi.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky