• Clinton da Trump sun samu nasara

  Hillary Clinton ‘Yar takarar neman shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrates da Donald Trump na Republican, sun yi nasara a zaben fitar da gwani da aka yi a cikin daren jiya, a mafi yawa daga cikin jihohi 12 na kasar.

  cigaba ...
 • George Bush ya yi wa kanin shi Kamfen

  Tsohon Shugaban kasar Amurka George Bush ya fito fili yana yi wa kanin shi Jeb Bush yakin neman zabe, inda ya bukaci Yan Jam’iyar Republican su goyawa ma shi baya maimakon wanda ke cika su da surutu.

  cigaba ...
 • Iowa: Ba zan yi kasa a gwiwa ba - Trump

  Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, ya ce bai damu ba duk da rashin nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na jam'iyyarsa da aka yi a jihar Iowa har sai ya kai ga nasara.

  cigaba ...
 • Trump ya ji tsoron shiga muhawara

  Mai neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya janye daga wata muhawarar da aka tsara za a yi ta gidan Talabijin din Fox.

  cigaba ...
 • IS ta yabama maharan da suka kai harin California

  Kungiyar ‘yan da’adda ta da’ish wadda aka fi sani da IS ta yaba amma kuma ba ta fito karara ta dauki alhakin kai hari kan wata cibiya a lokacin da wasu ke shan bidirinsu a Califonia lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane goma sha hudu.

  cigaba ...
 • Amurka za ta tura dakarunta zuwa Syria

  Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar da umurnin aikewa da dakarun kasar 50 zuwa Syria, karo na farko da Amurka ke tura sojojinta na kasa zuwa Syria tun daga lokacin da wannan rikici shekaru hudu da suka gabata.

  cigaba ...
 • AN GANA TSAKANIN SARKIN SAUDI AREBIYA DA SARKI SALMAN DA SHUGABAN AMURKA BARACK OBAMA

  A yau ne aka gana da shugaban kasar Saudi Salman bin Abdulaziz da kuma shugaban kasar Amurka Barack Obama a wata ziyara da y akai kasar AMruka ind asuka tattauna game da batun fadada yaki da suka ce suna yi da ta'adanci , har ila yau sun tattauna game da batun halin da ake ciki a kasar SIriya da Yaman , da kuma batun yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliyar kasar Iran, to sai dai wanna ganawa tana zuwa ne a daidai lokacin da kasar sausiya da kawayenta suke ci gaba da kai hare-haren ta'adancin kan fararen hula a kasar Yaman.

  cigaba ...
 • AN GUDANAR ZANGA-ZANGAR KIN JININ ZIYARAR NATANYAHO PIRA MINISTAN ISRA'ILA A BIRTANIYA

  Dubun dubatan alummar Birtaniya ne suka gudanar gagarumar zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da ziyarar da pira ministan Isra'ila Binyanmin Natanhu zai kai Birtaniya inda suka neman gwamnatin kasar da ta soke ziyarar tasa, tare da bayyana shi matsayin wanda ya tafka laifukan yaki, lamarin da gwamnatin tayi wasti da shi kuma ta nuna cewa bisa dokokin kasar duk wanda ya kawo mata ziyara to yana karkashin kulawarsu kuma za su bari a kama shi ba.

  cigaba ...
 • AN GUDANAR ZANGA-ZANGAR KIN JININ ZIYARAR NATANYAHO PIRA MINISTAN ISRA'ILA A BIRTANIYA

  Dubun dubatan alummar Birtaniya ne suka gudanar gagarumar zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da ziyarar da pira ministan Isra'ila Binyanmin Natanhu zai kai Birtaniya inda suka neman gwamnatin kasar da ta soke ziyarar tasa, tare da bayyana shi matsayin wanda ya tafka laifukan yaki, lamarin da gwamnatin tayi wasti da shi kuma ta nuna cewa bisa dokokin kasar duk wanda ya kawo mata ziyara to yana karkashin kulawarsu kuma za su bari a kama shi ba.

  cigaba ...
 • Dan bidinga ya kashe mutane a Amurka

  A kasar Amurka wani mutum mai shekaru 58 a duniya ya buda wuta a cikin wani gidan sinima inda ya kashe mutane biyu sannan ya raunata wasu 7, kafin daga bisani ya bindige kansa.

  cigaba ...
 • Amurka ta gargadi Amurkawa a Kenya

  Amurka ta gargadi ‘yan asalin kasarta da ke zaune a Kenya kan yiwuwar harin ta’addanci da za iya fuskanta gabanin ziyarar da Shugaba Obama zai kai a Kasar

  cigaba ...
 • Obama zai halarci jana'izar bakaken fata a Amurka

  Shugaban Amurka Barack Obama a ranar juma’a mai zuwa zai ziyarci garin Charleston na jihar Carolina, inda wani dan bindiga farar fata mai suna Dylaan Roof ya kai hari tare da kashe bakaken fata 9 a wata mujami’a.

  cigaba ...
 • An gurfanar da dan bindigar Charleston

  Wani abokin dan bindigar nan da ya harbe Amurkawa 'yan asalin Afrika a wani coci ya ce daama dan bindigar da ake tuhuma ya yi batun cewa yana son ya kashe wasu dalibai a wata Jami'a dake kusa da su.

  cigaba ...
 • Amurka za ta shigar da makamai a Iraqi

  A daidai lokacin da ya ke ci gaba da shan suka a ciki da waje sakamakon gazan kawo karshen yadda mayaka masu ikirarin jihadi ke ci gaba da kwace muhimman yankunan kasar Iraki daga hannun dakarunn gwamnati, shugaba Barack Obama ya ce Amurka za ta gaggauta bayar da horo da kuma manyan makamai ga wasu kabilun Iraqi domin kare kansu daga ‘yan bindiga.

  cigaba ...
 • Ana gasar zanen barkwancin Annabi{S.A.A.W} a Texas

  'Yan sanda a jihar Texas ta Amurka sun harbe wasu mutane biyu har lahira, wadanda suka bude wuta kan jami'in tsaro a wani wuri da ake gudanar da gasar nuna bajintar zanen-zanen barkwancin da aka kwaikwayi Annabi Muhammad (S.A.A.W).

  cigaba ...
 • Obama ya soki Firaminista Netanyahu

  Shugaba Obama ya zargi Firaministan HK Isra'ila Benjamin Netanyahu da sa a dauka cewa abu ne da ba zai taba yuwuwa ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Palasdinawa.

  cigaba ...
 • Obama: Babu wani sabon abu a jawabin Natanyahu

  Shugaba Barack Obama ya ce babu wani sabon batu da Firaminstan Hk Isra’ila Benjamin Natanyahu ya gabatar a jawabin da ya yi a zauren majalisar dokoki ta Amurka. Yayin da ya ke mayar da martini kan jawabin, Obama ya ce Natanyahu bai gabatar da wani shirin da ya fi inganci kan yadda za a magance matsalar kasar Iran ba.

  cigaba ...
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky