• Buhari ya mayar wa Atiku martani

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu wani lokaci da aka taba hana shi izinn shiga wata kasa a duniya, kamar yadda Mai Magana da Yawunsa Femi Adesina ya bayyana a wata sanarwa da ya aike wa BBC.

  cigaba ...
 • Bukin Maulidin Annabi (saw) A Nijeriya

  A cigaba da bukukuwan Maulidin Annabi (saw) a Nijeriya, a jiya 13 ga watan Rabi'ul Auwal 'yan darikun Sufaye da 'yan shi'a sun yi taruka da muzaharori domin murna da zagayowan wata da ranar haihuwan Annabi Muhammadu a garuruwa da dama a fadin tarayyan Nijeriya. Daga cikin garuruwan akwai Katsina, Minna, Suleja, Abuja da sauran wurare. Kuna iya ganin wasu hotuna da muka samo maku:

  cigaba ...
 • Jami’an Tsaro Sunyi Ruwan Barkonon Tsohuwa Akan Masu Maukibin Maulidi A Kaduna

  Jiya juma’a ce tayi daddai da 12 ga watan Rabi’ul Awwal wadda a irin wannan ranar ce aka haifi Annabi Muhammadu (saw) a garin Makkah a wani qaulin. Ya zama al’ada a tsakanin dukkan musulmin duniya -in ban da tsiraru- idan irin wannan rana ta zo su kan shirya gangami da taruka da walimomi da majalisosi na wa’azi domin girmama Manzon Allah (sawa) saboda murnar haihuwansa a irin wannan rana. Daga cikin wadanda suka fita jiya domin gangami da muzahara ta farin ciki domin murnan zagayowan ranar haihuwan Annabi a 12 ga watan Rabi’ul Auwal akwai ‘yan shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky a garuruwan da suka hada da Sokoto, Kano, Katsina, Bauci, Yola, Kauran Namoda, Talatan Mafara, Kebbi, da Zariya, Kaduna, da sauran wurare. A ko’ina an yi wannan gangami da muzahara lafiya in ban da Kaduna da Zariya in da jami’an tsaron ‘yan sanda suka yi kokarin tarwatsa wannan gangami da Muzahara. Mun samu labarin cewa masu muhazaharan ta Maulidi a Kaduna sun fara muhazaran ne daga randa ta ‘Leventis’ suna fadin ‘Labbaika Ya Rasulallah’ suna tafiya cikin tsari da natsuwa har zuwa wajen Kano Road sai ga ‘yan sanda sun zo suna ta an taya masu barkonon tsohuwa, amma bai hana cigaba da muzaharan ba. A wani kaulin an shaida ma majiyar mu cewa jami’an tsaron sunyi amfani da zaune gari banza domin afka ma masu muzaharan ta hanyar basu adduna da sanduna da makamai. Ya zuwa hada wannan labari bamu da cikakken bayani dangane da adadin wadanda aka raunata ko aka kama, amma babu labarin rasa rai. In ba a manta ba daman gwamnatin jihar Kaduna ta hana ‘yan dariku zagayen Maulidin da suka saba duk shekara, amma wai ta basu izini suyi gangami a Filin Taro na Murtala a ranar Lahadi. Mutane da dama suna ta Allah wadai da wannan yukuri na gwamnatin Kaduna. Akwai wanda ya shaida ma wakilinmu cewa yanzu ta bayyana gwamnati ba da ‘yan shi’a take fada ba, da musulunci take fada, saboda in ba haka yaya za a ce za a hana gangami da zagayen Maulidin Annabi? Ko Annabin na ‘yan shi’a ne?

  cigaba ...
 • Shi'a ta roki MDD da ICC kan Zakzaky

  Kungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya ta roki Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika da kuma Kotun Duniya da su tsoma baki wajen ganin cewa, gwamnatin Najeriya ta saki jagoransu, Sheik Ibrahim al-Zakzaky da matarsa da ke tsare kusan shekaru biyu.

  cigaba ...
 • Sabon shugaban Zimbabwe ya koma kasar jiya Laraba

  Mr. Emmerson Mnangagwa wanda shi ne mataimakin shugaban kasa kafin shugaba amaugabe ya tsigeshi abun da ya sa yayi gudun hijira, jiya ya koma kasar a matsayin sabon shugaban kasa biyo bayan matsin lambar da aka yiwa tsohon shugaban har yayi murabus

  cigaba ...
 • Jam'iyyar Mugabe na Zimbabwe na shirin tsige shi a yau

  A yayin da Jam'iyyar ZANU-PF mai mulki a Zimbabwe ke shirin tsige shugaba Robert Mugabe a Majalisar Dokokin kasar a yau Talata, mataimakin shugaban da aka kora daga mukaminsa, Emmerson Mnangagwa ya bukaci Mugabe da ya gaggauta sauka daga kujerar mulkin kasar.

  cigaba ...
 • Zimbabwe : Mugabe Ya Fito Bainar Jama'a

  A Karon farko tun bayan da sojoji suka kwace iko da wasu mahimman wurare a Harare babban birnin kasar Zimbabwe, shugaban kasar Rober Mugabe ya fito fili bainar jama'a

  cigaba ...
 • Mutane 18 sun mutu a harin Maiduguri

  Akalla mutane 18 sun rasa rayukansu yayin da 29 suka jikkata sakamakon wani hari da ‘yan kunar bakin wake suka kaddamar a yamamacin jiya a birnin Maiduguri da ke jihar Borno ta Najeriya.

  cigaba ...
Quds cartoon 2018
We are All Zakzaky