• Muzaharan Cika Shekara Biyu Da Ta'addancin Sojoji Akan Jagoran Harkar Musulunci A Nijeriya

  Daga cikin jerin tarukan da Harkan Musulunci ta shirya domin tunawa da harin ta'addancin da sojoji suka qaddamar akan jagoran Harkar musulunci Sheikh Zakzakyi a 12- 14 ga watan disambar 2015 akwai muzaharori da gangami da lekcoci da sauransu. A jiya Talata 12 ga watan disamba, almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun shiga birnin Abuja domin gabatar da muzaharan tunawa da harin sojoji akansu da kuma jaddada bugatansu na ya wajaba akan gwamnati ta bi umurnin kotu ta saki Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa wa'yanda suke a tsare tun bayan harin na disamba a hannun DSS. Majiyarmu ta shaida mana cewa jami'an tsaron 'yan sanda sun ja danga suna so su kawo wa wannan muzahara cikas.

  cigaba ...
 • ANYI MUZAHARAN ALLAH WADAI GAME DA YUNKURIN MAI DA HELKWATAR ISRA'ILA ZUWA BIRNIN QUDUS A NIJERIYA

  A jiya Juma'a ne, Yan Shi'a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky a Nijeriya suka yi muzahara da gangami domin nuna goyon baya ga Palasdinawa da kuma Allah wadai da yunkurin haramtacciyar kasar Isra'ila na mai da helkwatar kasar zuwa birnin Qudus. Anyi wa'yannan muzaharorin a garuruwan Kano, Gombe da sauran wurare a fadin tarayyan Nijeriya. In ba a manta ba a makon da ya gabata ne, shugaban kasar Amerika Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da amincewarsa na mai da helkwatar Isra'ila zuwa birnin Qudus da kuma bayyana aniyarsa na dauke ofishin jakadancin Amerika daga Tel'abib zuwa birnin Qudus.

  cigaba ...
 • An sace Shugaban PDP na Filato

  Wasu da ba Asan ko su wanene ba sun sace shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Filato Hon Damishi Sango tare da iyalan sa akan hanyar su ta zuwa Abuja domin halartar taron Jam’iyyar na kasa.

  cigaba ...
 • Shugaba Muhammadu Buhari Yana Ziyara Aiki A Kano

  A karon farko tun bayan kama rantsuwar aiki yau Laraba ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai fara ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar Kano, inda zai kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar Kano din ta kammala tare da aza harsashin wasu sabbi

  cigaba ...
 • Buhari ya mayar wa Atiku martani

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu wani lokaci da aka taba hana shi izinn shiga wata kasa a duniya, kamar yadda Mai Magana da Yawunsa Femi Adesina ya bayyana a wata sanarwa da ya aike wa BBC.

  cigaba ...
 • Bukin Maulidin Annabi (saw) A Nijeriya

  A cigaba da bukukuwan Maulidin Annabi (saw) a Nijeriya, a jiya 13 ga watan Rabi'ul Auwal 'yan darikun Sufaye da 'yan shi'a sun yi taruka da muzaharori domin murna da zagayowan wata da ranar haihuwan Annabi Muhammadu a garuruwa da dama a fadin tarayyan Nijeriya. Daga cikin garuruwan akwai Katsina, Minna, Suleja, Abuja da sauran wurare. Kuna iya ganin wasu hotuna da muka samo maku:

  cigaba ...
 • Jami’an Tsaro Sunyi Ruwan Barkonon Tsohuwa Akan Masu Maukibin Maulidi A Kaduna

  Jiya juma’a ce tayi daddai da 12 ga watan Rabi’ul Awwal wadda a irin wannan ranar ce aka haifi Annabi Muhammadu (saw) a garin Makkah a wani qaulin. Ya zama al’ada a tsakanin dukkan musulmin duniya -in ban da tsiraru- idan irin wannan rana ta zo su kan shirya gangami da taruka da walimomi da majalisosi na wa’azi domin girmama Manzon Allah (sawa) saboda murnar haihuwansa a irin wannan rana. Daga cikin wadanda suka fita jiya domin gangami da muzahara ta farin ciki domin murnan zagayowan ranar haihuwan Annabi a 12 ga watan Rabi’ul Auwal akwai ‘yan shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky a garuruwan da suka hada da Sokoto, Kano, Katsina, Bauci, Yola, Kauran Namoda, Talatan Mafara, Kebbi, da Zariya, Kaduna, da sauran wurare. A ko’ina an yi wannan gangami da muzahara lafiya in ban da Kaduna da Zariya in da jami’an tsaron ‘yan sanda suka yi kokarin tarwatsa wannan gangami da Muzahara. Mun samu labarin cewa masu muhazaharan ta Maulidi a Kaduna sun fara muhazaran ne daga randa ta ‘Leventis’ suna fadin ‘Labbaika Ya Rasulallah’ suna tafiya cikin tsari da natsuwa har zuwa wajen Kano Road sai ga ‘yan sanda sun zo suna ta an taya masu barkonon tsohuwa, amma bai hana cigaba da muzaharan ba. A wani kaulin an shaida ma majiyar mu cewa jami’an tsaron sunyi amfani da zaune gari banza domin afka ma masu muzaharan ta hanyar basu adduna da sanduna da makamai. Ya zuwa hada wannan labari bamu da cikakken bayani dangane da adadin wadanda aka raunata ko aka kama, amma babu labarin rasa rai. In ba a manta ba daman gwamnatin jihar Kaduna ta hana ‘yan dariku zagayen Maulidin da suka saba duk shekara, amma wai ta basu izini suyi gangami a Filin Taro na Murtala a ranar Lahadi. Mutane da dama suna ta Allah wadai da wannan yukuri na gwamnatin Kaduna. Akwai wanda ya shaida ma wakilinmu cewa yanzu ta bayyana gwamnati ba da ‘yan shi’a take fada ba, da musulunci take fada, saboda in ba haka yaya za a ce za a hana gangami da zagayen Maulidin Annabi? Ko Annabin na ‘yan shi’a ne?

  cigaba ...
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky