• Ministan Yada Labaran Nigeriya da Femi Adesina da Malam Garba Shehu Sun Ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a Ingila

  Femi Adesina a wata takarda da ya fitar yau Asabar,12 ga watan Agusta 2017,ya bayyana cewa yana cikin tawagar Ministan Yada labarai,Mr Lai Muhammad da suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a Ingila. A lokacin da Shugaba Buhari yake masu bayani dangane cigaban da ya samu dangane da lafiyarsa ya bayyana masu cewa: "Alhamdulillah,na samu sauki sosai dangane da rashin lafiya ta,kuma ina son in dawo gida,amma dai na ga ya fi dacewa in bi umurnin likita na,ba wani ba saboda shike da cikakken masaniya dangane da abinda ya kamata na yi."in Shugaba Buhari. In ba a manta ba,Shugaba Buhari ya kwashe fiye da kwanaki 90 a Ingila domin ganin likitansa,wanda wannan ya haifar da taqaddama tsakanin mutanen Nigeriya.

  cigaba ...
 • Hotunan zanga-zangar neman Buhari ya yi murabus

  Wasu kungiyoyin al'umma sun yi zanga-zanga suna kira ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka. A ranar Litinin ne wasu kungiyoyin al'umma suka yi zanga-zanga suna kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka. Masu zanga-zangar sun ce sun shirya ta ne ganin cewa shugaba Buhari ya shafe kwanaki 92 yana jinya a birnin London, kuma har yanzu babu wani bayani kan yanayin rashin lafiyarsa ko kuma lokacin da zai koma bakin aiki. Wani mawaki mai suna Charly Boy ne ya shirya zanga-zangar wacce ba ta samu halartar mutane da dama ba. Mutanen sun yi ta daga kyallaye da ke dauke da rubuce-rubuce da dama na neman shugaban ya sauka daga mulki. Gomman masu zanga-zangar sun faro ne daga dandalin Unity Fountain da ke birnin tarayya Abuja, inda suka dire a kwanar shiga fadar shugaban kasa, bayan da jami'an tsaro suka dakatar da su. Daga cikin kungiyoyin da suka halarci zanga-zangar har da kungiyar 'yan uwa Musulmai ta Shi'a da ke kira da a saki shugabanta Malam Ibrahim El-Zakzaky MAsu zanga-zangar dai sun ce za su ci gaba da yin zaman dirshan a wajen har sai sun ga abin da ya turewa buzu nadi

  cigaba ...
 • Babban taron tunawa da haihuwar Imam Ridha[AS] na shekara shekara a Kano

  Ana gayyatar daukakin al'ummar musulmi zuwa babban taron tunawa da haihuwar limami na takwas cikin jerin limaman shiriya na gidan Manzon Allah[SAWA] watau Imam Ali Ibn Musa Arridha[AS] wanda Harkar Musulunci ta saba gabatarwa a ko wacce shekara. A wannan karon za'a gabatar da wannan babban taro ne a Kano......................, Malam Sunusi Abdulkadir shine mai masaukin baki. Da yardan Allah za'a kwashe tsawon kwanaki uku ne ana gabtar da taron inda za'a soma shi tun daga ranar Alhamis zuwa ranar Asabar in Allah ya yarda

  cigaba ...
 • Wasu ‘Yan Biafra sun yi ikirarin kafa gwamnati

  Shugaban wata kungiya a kudancin Najeriya da ake kira Biafra Zionist Federation Benjamin Onwuka ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasar Biafra na riko, tare da zayyana sunayen ministocin sabuwar gwamnatinsa

  cigaba ...
 • Manyan Hafsoshin mayakan Najeriya Sun Isa Birnin Maiduguri.

  Manyan hafohin mayakan Najeriya sun isa birnin Maiduguri a jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria biyo bayan umarnin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo cewar manyan sojojin su koma yankin da ya sha fama da hare haren yan ta’addan Boko Haram tare da yin garkuwa da mutanen yankin.

  cigaba ...
 • Hajji 2017: Jirgin farko ya tashi da Mahajjatan garin Abuja zuwa kasa mai tsarki daga Nigeriya

  Yau Lahadi,30 ga watan Yuli,2017,da misalin karfe 15:16 agogon Nigeriya, jirgin farko ya tashi da mahajjatan daga filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja tarayyar Nigeriya zuwa kasa mai tsarki. An fara jigilar Alhazan ne da mahajjatan garin Abuja wadanda ake sa ran zasu sauka a filin jirgin saman Sarki Muhammad bn AbdulAziz dake Madina.Kimanin mahajjata 460 ne suka tashi daga Abuja zuwa kasa mai tsarki,maza 299,mata 161. Shugaban Hukuman Hajji ta kasa,Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad,a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen fara jigilar Alhazan, ya bayyana cewa kimanin mahajjata dubu saba’in da tara ne ake sa rai zasu je kasa mai tsarki domin aikin hajji a bana. Barista Mukhtar yayi kira ga mahajjatan da su zama jakadu na gari ga wannan kasa ta hanyar bin dokokin da ka’idojin kasa mai tsarki a lokacin da suke kasa mai tsarki domin aikin hajji

  cigaba ...
 • Hardace Alkur’ani ga yara abin farin ciki ne da Murna _____Inji Sheikh Yakubu Yahaya Katsina

  Yau Asabar 22 ga watan Yuli 2017 ne,Fudiyya Tahfiz Kano ta yi bukin yaye dalibai mahaddata Alkur’ani a filin Dantata dake Dandishe Kano. Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a lokacin da yake gabatar da jawabi a matsayin babban bako a wajen bikin ya bayyana cewa hardace Alkur’ani ga yara abin farin ciki ne da murna. Malamin yayi nasiha da jan hankali ga daliban da suka haddace Alkur’anin da kuma Malaman su daliban.Sannan ya nuna muhimmancin samar da makaranta ta tafsirin Alkur’ani mai girma domin ka da a bar yaran su tafi haka nan don sun yi sauka. Sannan ya tabbatar da cewa a cikin rahoton da turawan mulkin mallaka suka kaiwa iyayen gidansu,akwai cewa yankin gabas (Borno)wuri ne da ake samun ilmin Alkur’ani shi yasa ake neman tarwatsa yankin.Yanzu ta bayyana karara ana fada da Alkur’ani ne,sannan ita kuma hukuma tana so ta kashe tasirin karatun Alkur’ani a cikin al’umma. Malamin yayi kira ga mawadata a cikin harka da su taimaka ma makarantun Fudiyya,yana cewa: “Su Malam na fada mana cewa mutum ya kure iyakar abinda yake iya yi domin neman sakamako a lahira.” Ya kara da cewa: “Su Sayyida sun bada lakani cewa idan kana bayarwa (wato infaqi) to Allah zai nunnuka maka abinda kake bayarwa din.” Sannan Malamin ya kirayi ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky da suyi ilimin boko amma lokaci guda kada a bar ilimin Alkur’ani domin dukkansu ilimi ne kuma ana yin ilimi domin Allah ne.Yana cewa: “Shi karatu ana yinsa domin Allah ne,idan aka cire Allah a cikin karatu,to,komai sai ya dame ma mutum.” A karshe yayi kira da ‘yan uwa su hada kansu yana cewa: “Mu kara riko da junan mu,mu girmama ra’ayin juna.Duk ayyukanmu na gayya ne,duk inda muke mu yiwa juna uzuri.A iya sani na babu wani dan uwa wanda yake wani aiki don rugujewar harka,kowa na yin iya kokarinsa domin cigaban harka.” Bukin ya samu halartan wakilan ‘yan uwa na garuruwa da dama da sauran ‘yan uwa daga sassa daban daban na kasan nan.

  cigaba ...
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky