WASU MALAMAN SUNNAH SUN CE WANDA DUK YACE BA ZA A AZABTAR DA IYALIN ANNABI BA, TO, YA ZO DA BAKIN SHI’ANCI

WASU MALAMAN SUNNAH SUN CE WANDA DUK YACE BA ZA A AZABTAR DA IYALIN ANNABI BA, TO, YA ZO DA BAKIN SHI’ANCI

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a lokacin da yake gabatar da karatun littafin Muqaddimatul Azeefa na ranar Juma’a, 27/4/2018, ya bayyana cewa su makiya iyalan Annabi (sawa) in baka yarda da cewa iyalan Annabi (sawa) in sun rasu- ko da sun mutu a kan tauhidi- yan wuta ne ana babbaka su a wuta ba, to, kai bakin dan shi’a ne (wato Rafidiy).

Malamin yace:
 “ Wa’yannan mutane babu wani farin ciki a gunsu illa a ce a azabtar da iyalan Manzon Allah (sawa), sannan zasu ji dadi su ce Allah ya saka maka da alkhairi, kai mumini ne mutumin kirki. Ta yaya ba za a yi haka ba? Bayan an shekara dari a Sham ana cewa Allah ka tsinewa Ali, Allah ka tsinewa AlHasan da Husaini, Allah ka tsinewa sirikin Manzon Allah mijin Fatima, jama’a kuma suna cewa Ameen. Ta yaya ba za a yi haka ba? Wanda suke wannan sune Ahlus Sunnah.
 “ (Iyalan Annabi) ko da sun mutu akan tauhidi- abinda suke so ko sun mutu a kan tauhidi a kona su. Wanda duk yace ba za a azabta iyalan Annabi ba, to ya zo da bakin shi’anci, ya zo da bala’I, don haka ko mutuwa yayi kar kace Allah ya ji kansa. Akwai wanda yake gaya min cewa ba tun yau wannan mutumin yake dauke da wannan masifar ba, ya dade dauke da abarsa saidai Allah ya yaye domin ni na ji shi yana cewa shi ya dauki layin hada kan musulmi ba ruwansa da wane bangare kake, kai abokin tafiyarsa ne, ko a ina kake, da waye ba zai hada kai ba? Yace da dan shi’a. Kowace irin firqa kake ni zan iya hada kai da kai sai dan shi’a. To, abin mamaki da ya tashi bada hujjarsa akan cewa dukkan musulmi zai hada kai dashi sai ya bada hujja da hikayar Annabi Harun yayan Annabi Musa da waqi’ar bautan maraki da Banu Isra’ila suka yi yayin da ya tafi ganawa da Allah. Yace ku gane munin rabuwar kai, Annabi Harun yayi wa Annabi Musa uzuri bisa kyale Bani Isra’ila suyi shirka su bautawa maraki saboda kai ya raba kai. Da ya zo yace AFA ASAITA AMRIY, saba min kayi? Me yasa kaga sun batar baka tsawatar ba?INNI KASHITU AN TAKULA FARRAQTA BAINA BANU ISRA’ILA, na ji tsoron ka da kace min ka raba kan banu Isra’ila, shi yasa na kyale su suyi shirka. Ku duba wannan zance.
 “ Wato, anan yana nuna, hujjar da yake kafawa in aka bi ta kan hujjar Kenan gwamma mushriki da wanda ya nasabta kansa da Ahlulbait. Domin ga hujjar da yake bayarwa cewa Annabi Haruna yana wa Annabi Musa uzuri da kyalewa a yi shirka don kada kai ya rabu. Shi kuma yana cewa in kana shi’a ba zai hada kai da kai ba, zai raba kai da kai, wato gwamma mushriki kenan dan shi’a a gunsa. Zai iya hada kai da mushriki Kaman yanda yake gashi mun gani. Ana cewa da Allah mutumin banza bai ce uffan ba, yana cewa zai yi majalisi takwas kan Mu’awiyyah. Ka ga ya hada kai da wa? Da mushrikai masu zagin Allah, don bamu ji me yace, kuma bai taba majalisinsa kansu ba, kuma na tabbata yanda yake da ‘yan tsegumi duk abinda aka yi ya ji a kunnensa illa shi yana da hujjar Annabi Haruna ya yarda an yi shirka don kai ya hadu. Don haka shima yanzu Sarkin tsantseni ya yarda a yi shirka don kai ya hadu, abinda bai yarda a yi ba shine shi’a. Allah ka yayewa al’umma. Shekaranjiya wani yake ban wannan maganar mai sa a yi kuka da hawayen jinni.
 “ Don haka, idan mutum ya kalli abinda Zahabi yayi da ya zo takhrijin wannan hadisi zai bashi tsoro cikin talkisin da ya yiwa Mustadrak, zaka dimauta matuka. Ku duba iya maganar dake ciki, babu alfarman kowa bare sahabi, kuma falalan ba wata falala ce ta daban ba, ta kowa ce, aka fade ta kan iyayen dakinmu, ‘ya’yan Annabi, amma Zahabi bai iya kyale hadisin nan ba saida ya iyar mai, don me za a ce duk sharifin da ya mutu kan tauhidi da Imani da manzancin Annabi dan aljanna ne? Sai ya dau mashi ya burma hadisin. Sai Zahabi yace hadisi ne mummuna bai inganta ba- ku duba lafazin farko, yace mummuna ne. Cewa duk sharifin da ya mutu kan Imani da Annabi ba za a yi me azaba. Zahabi yace mummunan hadisi ne. Meye kyakkyawan hadisi? Shine Sharifi ko ya mutu akan tauhidi sai an babbaka shi, sai a ce Alhamdulillah zance yayi kyau an babbaka matsiyata. Wai kuma wa’yannan su ake ta yakata akan yakar su da nake.”


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky