Zarif: Bakar Farfangar MOSSAD A Kan Iran Ba Zai Bakanta Alakar Iran Da Kasashen Duniya Ba

Zarif: Bakar Farfangar MOSSAD A Kan Iran Ba Zai Bakanta Alakar Iran Da Kasashen Duniya Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar kokarin bakanta sunan Iran da kungiyar leken asirin haramtacciyar kasar Isra'ila (MOSSAD) take a idon duniya ba zai yi nasara wajen bata alakar da Iran take da shi da kasashen duniya ba.

Ministan harkokin wajen na Iran, ya fadi hakan ne a matsayin mayar da martani ga kokarin MOSSAD din na bata alakar da ke tsakanin Iran da kasar Denmark biyo bayan wani zargi da kasar Denmark din ta yi na cewa Iran tana kokarin kashe wani dan adawar kasar a kasar Denmark din lamarin da Iran ta musanta.

Dakta Zarif ya ce akwai hannun kungiyar ta MOSSAD cikin wannan sabon makircin wanda ya ce hakan ba zai cutar da alakar da ke tsakanin Iran da sauran kasashen duniya ba.

A kwanakin baya ne dai kasar Denmark din ta sanar da kama wani mutum dan asalin kasar Iran tana mai zarginsa da kokarin kai hari da kisan gilla a cikin kasar. Daga baya kungiyar ta MOSSAD ta fitar da sanarwar cewa tana da hannu cikin ba da bayanan sirri da suka kai aka kama mutumin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky