Zanga-Zangar Neman Sakin Sheikh El-Zakzaky A Najeriya

Zanga-Zangar Neman Sakin Sheikh El-Zakzaky A Najeriya

Al'ummar musulmi mabiya mazhabar Shi'a almajiran sheikh Ibrahim Elzakzaky na ci gaba da gudanar da zanga -zanga neman a saki jagoran na su domin yi masa magani

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewa a jiya Litinin duban al'ummar musulmi mabiyar mazhabar shi'a  ne suka gudanar da zanga-zanga a biranan  Zariya da Abuja, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta bi umarni kotu ta kuma saki sheikh Zakzaky domin a fitar da shi kasashen waje a duba lafiyarsa,

Kafin hakan dai a jiya lahadi, an gudanar da irin wannan zanga-zanga a birane da dama na kasar ciki kuwa har da birnin kaduna, inda jami'an 'yan kasar suka kashe mutum guda daga cikin mahalarta zanga-zangar.

Zanga-zangar dai ta biyo bayan wasu labarai ne da suke nuna cewa, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya din Sheikh Ibrahim El-Zakzaky yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya, a inda ake tsare shi, da yake bukatar kula ta likitoci na gaggawa. Don haka masu zanga-zangar suka kira gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gaggauta sako shi don fita da shi wajen kasar don sama masa kula ta musamman cikin gaggawa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky