Zamfara: 'Yan bindiga sun hallaka rayuka 1,321 cikin shekaru 7

Zamfara: 'Yan bindiga sun hallaka rayuka 1,321 cikin shekaru 7

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Alhaji Sanusi Rikiji, ya ce mutane dubu 1,321 ‘yan bindiga suka hallaka kama daga shekarar 2011 zuwa yanzu, yayin da 'yan bindigar suka jikkata wasu mutanen dubu 1,881.

Rikiji wanda shi ne shugaban wani kwamiti da aka dorawa alhakin tance tance barnar da ‘yan bindiga suka yi jihar ta Zamfara da kuma bada tallafi, ya ce sama da shanu dubu 10,000 barayi suka sace, yayin da suka lalata gonaki da fadinsu yakai kadada dubu 2,688 sai kuma gidaje 10,000 da hare-haren ‘yan bindigar suka lalata tun daga shekarar ta 2011 zuwa yanzu.

Kakakin majalisar ya bayyana haka ne, yayin ganawa da kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa a karkashin gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi, wada ya ziyarci jihar ta Zamfara a ranar Asabar.

Sanusi Rikiji ya ce gwamnatin jihar ta Zamfara ta yi shirin taimakawa wadanda hare-haren ‘yan bindigar ya shafa da iyalansu tallafin rage radadin hasarar da suka tafka.

A gefe guda kuma, kwamitin da jihar Zamfara ta kafa, wanda ta dorawa alhakin sulhu da kungiyoyin ‘yan bindiga da kuma sauya musu dabi’u, ya ce zuwa yanzu an samu nasarar shawo kan akalla dubu 3,000 ne suka tuba daga cikin gugun ‘yan bindiga a jihar, bisa tallafawar Wakilan gwamnati, jami’an tsaro da kuma Sarakunan Gargajiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky