Yukiya Amano Ya Jaddada Cewa Iran Tana Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya

Yukiya Amano Ya Jaddada Cewa Iran Tana Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya

Shugaban hukumar makamashi ta kasa da kasa Yukiya Amano ya ce; Fiye da shekaru biyu kenan da hukumar take sanya idanu kusa da kuma akan aiki da yarjejeniyar ta Nukiliya

Yukiya Amano ya yi ishara da matsin lambar Amurka akan yarjejeniyar da zummar rusa ta, sannan ya kara da cewa: Rushewar yarjejeniyar wata asara ce mai girma.

Amano ya kara da cewa Hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa za ta ci gaba da aikinta domin tabbatar da ganin cewa Iran din tana aiki da yarjejeniyar.

Daga kulla yarjejeniyar Nukilar zuwa yanzu, hukumar makamashin Nukiliya ta fitar da rahotanni tara akan yadda Iran din take aiki da yarjejeniyar.

A watan Janairu na 2016 ne aka fara aiki da yarjejeniyar Nukiliyar da aka cimmawa a tsakanin Iran da Kasashen Rasha, China, Birtaniya, Faransa, Amerika da kuma kasar Jamus


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky