Yemen: An Kashe Tsohon Shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh

Yemen: An Kashe Tsohon Shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh

Rahotanni daga Yemen sun ce an kashe tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh a yau a lokacin da yake shirin tsrewa daga San'a zuwa Maariba.

Shafin yada labarai na Saba'a net ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar harkokin cikin gida a kasar Yemen ya tabbatar da mutuwar Ali Abdallah, wanda aka kashe shi a lokacin da yake shirin tserewa zuwa yankin Maarib domin tsallakawa cikin kasar hadaddiyar daular larabawa.

Gwamnanan na San'a ya tabbatar da cewa masu yunkurin haifar da fitinar sun tsere daga wuraren da suka kafa tungarsu a cikin birnin da ma sauran birane.

Inda ya ce yanzu haka jami'an tsaro ne suke rike da dukkanin wuraren da 'yan bindiga magoya tsohon shugaban kasar suka mamaye a ranar Laraba da ta gabata, yayin da wasu daruruwa daga cikinsu suka mika kansu da makaman da ke hannunsu.

Rundunar sojin kasar Yemen tare da taimakon dakarun sa kai na kabilun larabawan Yemen sun samu nasarar murkushe boren da tsohon shugaban kasar ta Yemen Ali Abdallah saleh ya tayar, da nufin bayar da dama ga kasashen da ke yaki da al'ummar Yemen su samu damar kwace birnin San'a, hakan yana faruwa ne tare da taimakon gwamnatin UAE lamarin bai yi nasara ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky