Yau Za A Yi Zanga-Zanga A Birnin New York Kan Kalaman Trump Game Da Afirka

Yau Za A Yi Zanga-Zanga A Birnin New York Kan Kalaman Trump Game Da Afirka

Ana cigaba da nuna bacin rai game da kalaman batuncin da aka danganta su da Shugaban Amurka Donald Trump. Ko a yau dinnan Litini, yayin da ake bukukuwan zagayowar ranar tunawa da dan raji Martin Luther King Jr a fadin Amurka, a Birnin New York wannan bukin zai hada da yin zanga-zangar nuna bacin rai kan kalaman na Trump

Tun bayan da aka yi zargin cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da kalamai marasa dadi kan tsiraru, musamman ma wadanda su ka fito daga Afirka da Haiti, aka shiga nuna bacin rai. Hasali ma an yi ta bayyana Trump da mai nuna wariyar launin fata saboda wannan zargin. To sai dai Trump ya ce an yi karin gishiri akan ainihin abin da ya fada. Ya ce shi abin da ya yi kokarin nunawa shi ne cewa, ya kamata kowa ya shigo Amurka bisa cancanta amma ba bisa wata alfarma ba. To saidai wannan bai hana mutane cigaba da nuna bacin rai ba.

Ko a yau dinnan an shirya za a yi zanga-zanga a Birnin New York ta nuna bacin rai kan wadannan kalaman da ake tanganta su da Trump. Zanga-zangar, wadda za a yi ta albarkacin zagayowar ranar tunawa da marigayi Martin Lurther King, za ta samu halartar kungiyoyi da dama na rajin kare hakkin dan adam da kuma jinsunan tsiraru dabam dabam. Saboda haka abokiyar aikinmu Alheri Grace Abdu ta tattauna da wani shugaban al’umma dan asalin kasar Ghana mai suna Muhammadu Mada, wanda ya ce kalaman da aka danganta su ga Trump sun yi kama da abin da Trump zai iya fadi.

Malam Mada ya kara da cewa kungiyar kasashen Afirka ta AU ta rubuta takardar nuna bacin rai ga Ofisoshin Jakadancin Amurka da ke kasashe dabam dabam. Ya ce kamar yadda duniya baki daya ta yi Allah wadai da wadannan kalaman, ‘yan Afrika da ke Amurka su ma sun yi Allah wadai da kalaman. Da aka yi nuna da cewa wasu da ke wurin sun ce ba haka Trump ya fad aba, sai Mada ya ce take-taken Trump a baya sun nuna cewa shi mutum ne da zai iya furta irin wadannan kalaman.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky