Yanzu Haka Ina Babbar Kotu da take a    N D A, Kaduna:

Yanzu Haka Ina Babbar Kotu da take a    N D A, Kaduna:

Wata Babbar Kotu ta Bayar da umarnin Garkame tsohon Gwamnan jahar Kaduna a Gidan Yari tare da mutun uku:

 Babbar kotun dake Jihar Kaduna ta bayar da Umarnin aci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin inuwar jam'iyyar PDP Muktar Ramalan Yaro.


Haka kuma kotun ta kuma bayar da Umarnin tsare tsohon  Ministan Lantarki na Jiha Nuhu Wya da tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna Hamza Ishaq Dan mahawayi da kuma tsohon ciyaman na Jam'iyyar (PDP)Haruna Gaya.


Kotun kolin Jihar Kaduna tana tuhumar tsofaffin shugabanin da laifukan da suka shafi cin amanar kasa wawushe dukiyar Al'umma  da kuma aikata almundahana.


Mai Shari'a Mohammed Shuaibu shiya bayar da Umarnin tsare su bayan karbar rahoton hukumar (EFCC).


Duk da dai lauyan Muktar Ramalan Yaro ya bukaci a bashi belin tsohon Gwamnan domin ya tafi dashi gida,sai dai alkalin yayi burus da bukatar haka.


 Alkalin kotun ya bayar da umarnin  tasa keyar tsohon Gwamnan da mutun uku da ake tuhumarsu zuwa gidan yari har zuwa Ranar Alhamis mai zuwa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky