'Yan Uwa Musulmi Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman Sakin Sheikh Zakzaky

'Yan Uwa Musulmi Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman Sakin Sheikh Zakzaky

Yan uwa uwa musulmi almajiran sheikh Ibrahim Yakubu Elzakzaky sun gudanar da gagarimar zanga-zangar neman gwamnati ta sako jagoransansu da kuma nuna fishin kan harbin da jami'an tsaro suka yi wa Malam Qasim Umar shugaban 'yan uwa musulmi na jahar Sakoto da ya yi sanadiyar shahadarsa.

A jiya Litinin, 'yan uwa musulmi mabiya mazhabar shi'a almajiran sheikh Ibrahim Yakubu Elzakzaky da suka fito da jahohin kasar sun gudanar da gagarumar zanga-zanga zuwa gaban ofishin kare hakin bil-adama ta kasar dake birnin Abuja inda suka bukaci kungiyar ta tilastawa gwamnatin kasar ta gudanar da adalci kan wadanda suka harbi marigayyi Sheikh Kasim Umar.

A zanga-zngar neman sakin Shekh Ibrahim Elzakzaky makoni uku da suka gabata da aka yi a birnin Abuja, jami'an 'yan sanda suka halbi marigayi Malam Qasim Umar a tsinyarsa, bayan kwashe makoni biyu yana jiya marigayin ya yi shahada.

Har ila yau mahalarta zanga-zangar sun bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin Sheikh Ibrahim Yakubu Elzakzaky tare da mai dakinsa kamar kotun ta bayar da umarni. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky