'Yan Shia Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky Sunyi Taron Arba'in A Abuja

'Yan Shia Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky Sunyi Taron Arba'in A Abuja

Yau Juma'a 10 ga watan Nawumba, 'yan Shia mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky suka yi taron Arba'in na shahadar Abu Abdillahil Husain da zanga zangar neman gwamnati da ta gaggauta sakin jagoransu Sheikh Zakzaky wanda ya kusa cika shekaru biyu a tsare duk da umurnin kotu da a sake shi.
'Yan Sanda sun yi kokarin tarwatsa masu zanga zangar ta hanyar harba ma masu zanga zangar barkonon tsohuwa amma duk da haka sai da suka isa in da suke so su isa da zanga zangar.
Ya zuwa hada wannan labari babu rasa rayuka amma akwai wa'yanda suka samu rauni.
An rufe zanga zangar ne a farfajiyar Fountain dake Abuja.

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky