'Yan Sandan Nijeriya Sun Yi Harbi Kan Masu Muzahara kan A Saki Sheikh Zakzaky Domin Ya Nemi Magani

'Yan Sandan Nijeriya Sun Yi Harbi Kan Masu Muzahara kan A Saki Sheikh Zakzaky Domin Ya Nemi Magani

'Yan Sanda a Nijeriya sun yi ruwan harsasai masu rai a kan masu jerin gwano domin a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky Yau Laraba a Abuja babban birnin tarayyan Nijeriya.
Yau ce rana ta uku cikin jerin kwanuka da almajiran Sheikh Zakzaky suke fitowa suna jerin gwano domin neman gwamnatin Nijeriya da ta bi umurnin kotu ta saki jagoran nasu wanda a halin yanzu yake cikin matsanancin halin rashin lafiya.
Wakilinmu ya shaida mana cewa a wajajen Area 10 dake Abuja ne a lokacin da masu muzaharan suke tafiya cikin tsari da lumana suna wakoki na kira ga gwamnati ta saki jagoransu domin neman magani sai kawai 'yan sanda suka fara ruwan barkonon tsohuwa da harsasai masu rai ga masu muzaharan lumanan.
Ya zuwa hada wannan labarin mutum daya ne kawai muke da labarin an kashe a lokacin, sai dai an raunata da dama, kuma an kama da dama.
Mutane da dama suna ta Allah wadai da wannan aika aika na yan sandan Nijeriya.

Abuja

Abuja

Abuja

Abja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky