'Yan Sandan Iran Sun Cafke Wasu Manya Da Ga Cikin Masu Tayar Da Fitina

'Yan Sandan Iran Sun Cafke Wasu Manya Da Ga Cikin Masu Tayar Da Fitina

yan sandan kasar Iran sun bayyana cewar jami'an su sun samu nasarar ganowa da kuma kame dukkanin wadanda suka tsara da kuma aiwatar da rikice-rikicen da ya faru na baya-bayan nan a wasu garuruwa na kasar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Janar Saeed Montazer al-Mahdi ya bayyana hakan a yau din nan Lahadi inda ya ce tuni aka samu nasarar gano da kuma kame manyan wadanda suke da hannu cikin tashin tashinan da ta faru a wasu garuruwa na Iran yana mai cewa a halin yanzu dai an kawo karshen rikicin hankula duk sun kwanta a wadannan garuruwa.

Janar Montazer al-Mahdi ya kara da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar bambance tsakanin masu zanga-zanga na gaskiya wadanda suke da korafi da kuma masu tada tarzoma wadanda suka karya doka, inda tuni aka kama su.

Kakakin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kama din har da wadanda suka kona tutar Iran da kuma wadanda suka sanya wa wata motar 'yan kwana-kwana wuta a garin Doroud lamarin da yayi sanadiyar mutuwar wani mutum da dansa, yana mai cewa kimanin mutane 20 ne suka rasa rayukansu ciki kuwa har da wani jami'in 'yan sanda. Jami'in ya kara da cewa tuni aka mika wadanda aka kama din ga ma'aikatar shari'a wacce ta sake da dama daga cikinsu sauran wadanda suke da hannu cikin tarzomar kai tsaye kuma ana ci gaba da rike su don yi musu shari'a.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky