Yan sanda sun kama Sanata Omo-Agege

Yan sanda sun kama Sanata Omo-Agege

Jami’an ‘yan sanda sun kama Sanata Ovie Omo-Agege, bayan hatsaniyar da magoya bayan sa suka tayar inda suka kutsa cikin zauren Majalisar Dattawa suka arce da Sandar Mulki

An kama Sanatan ne a harabar Majalisar Tarayya inda aka fice da shi a cikin bakar mota kirar Totota Hilux da misalin karfe 1:54 na ranar yau Laraba.
Bayan hatsaniyar dai Omo-Agege ya koma cikin zauren majalisar.
A safiyar yau Laraba ne masu zanga-zanga suka kutsa cikin zauren Majalisar Dattawa, suka tada hargitsin da har su ka sace sandar mulkin majalisa.
Ana kyautata zaton masu zanga-zangar magoya bayan Sanata Ovie Omo-Agege ne, wanda aka dakatar cikin makon da ya gabata saboda zakalkalewar da aka ce ya yi wajen zargin majalisa da kokarin kulla wa Shugaba Buhari gadar-zare ta hanyar yunkurin da aka yi na sauya ranakun gudanar da zaben 2019.
Wannan sandar dai ita ce alamar daraja da martabar Majalisar Dattawa, kuma ita ce tambarin karfin ikon majalisar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky