Yan bindiga sun kutsa kai cikin wata cibiyar horar da jami’an soji a Kabul

Yan bindiga sun kutsa kai cikin wata cibiyar horar da jami’an soji a Kabul

Wa yan bindiga dauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin wata cibiyar horar da jami’an soji dake Kabul a kasar Afghanistan, inda suka yi ta dauki ba dadi tsakanin su da jami’an tsaro.

Kakakin yan Sandan birnin Bashir Mujahid ya bayyana cewar an ji karar makamin roka da kuma bindigogi a cikin Cibiyar da ake kira Marshal Fahim Military Academy.

Bayanai sun ce an hallaka mutane da dama a harin dake zuwa kwana guda bayan wani kazamin harin da ya hallaka mutane sama da 100 a birnin.

Kungiyar Isil ta sanar da daukar alhakin kazamin harin Cibiyar horar da soji na Kabul a Afghanistan


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky