Yahudawan Sahayoniya Sun Mayar Da Birnin Kudus Sansanin Soja

Yahudawan Sahayoniya Sun Mayar Da Birnin Kudus  Sansanin Soja

Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun mamaye birnin Kudus domin hana palasdinawa Isa masallacin kudus.

Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun mamaye birnin Kudus  mako daya bayan  hana palasdinawa yin salla a masallacin kudus.

Tun da safiyar yau ne sojojin yahudawan su ka kafa shinge na karfe a kofar  Babul Asbat ta masallacin kudus, kamar kuma yadda su ka mamaye duk wasu hanyoyin da su ke isa zuwa ga masallacin.

Rahotanni daga kudus sun cewa; 'yan sahayoniyar sun girke sojoji 2000 a cikin birnin na Kudus.

Dubban palasdinawa da su ka ki amincewa da su bi ta cikin kofar bincike da 'yan sahayoniyar su ka kafa a bakin masallacin kudus.

A wasu sassa-sassa daban-daban na palasdinu an yi taho mu gama a tsakanin samarin palasdinawa da kuma sojojin sahayoniya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky