Wasu Mahara sun kashe mutane 27 a Najeriya

Wasu Mahara sun kashe mutane 27 a Najeriya

Wasu yan bindiga dauke da makamai sun kai kazamin hari karamar hukumar birnin Gwari dake Jihar Kadunan Najeriya inda suka kashe mutane 27.

Daya daga cikin shugabanni yankin Zubair Idris Abdurauf yace an kai harin ne daren jiya asabar a kauyen Gwaska da Kuiga Inda aka kashe mazauna garuruwan harda kananan yara.

Shugaban yankin Zubair dris yace maharan sun fito ne daga jihar Zamfara kuma harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan Sufeto Janar na yan sanda Ibrahim Idris ya ziyarci garin Inda ya sanarda tura karin yan Sanda 200.

Babu karin haske kan ainahin dalilin kai wannan hari, a baya bayan nan dai yankin birnin Gwari da ke jihar Kaduna ya sha fama da hare-haren 'yan bindiga, matsalar da gwamnatin jihar da ta tarayyar Najeriya suka sha alwashin kawo karshenta.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky