Wasu Gungun 'Yan Majalisa Nigeria Sun Nesanta Kansu Daga Sharuddan Da Majalisar Ta Kafa Wa Buhari

Wasu Gungun 'Yan Majalisa Nigeria Sun Nesanta Kansu Daga Sharuddan Da Majalisar Ta Kafa Wa Buhari

Wasu gungun 'yan majalisar dattawa da ta wakilan Nijeriya sun nesanta kansu daga sharuddan da a jiya majalisar ta kafa wa shugaban kasar Muhammadu Buhari ko kuma su dau mataki kansa, suna masu jaddada goyon bayansu ga shugaban.

A wata sanarwa da wadannan gungun 'yan majalisar dauke da sanya hannun Hon. Abdulmumin Jibrin, daya daga cikin 'yan majalisun wakilan Nijeriya, sun bayyana cewar akwai wata mummunar manufar cikin sharuddan da majalisun biyu suka kafa wa shugaba Buharin a jiya suna masu cewa mafi yawa daga cikin abubuwan da suka zo cikin sharudda tuni an tattauna kansu a majalisar.

Har ila yau sanarwar ta kirayi 'yan majalisar da kada su yi abin da zai haifar da rikici da rarrabuwan kai a kasar kamar yadda suka kirayi 'yan majalisar da suke fuskantar shari'a saboda zargin rashawa da cin hanci ko sauran laifuffuka da su magance matsalarsu ta hanyoyin da suka dace ba tare da shigo da majalisa cikin lamarin ba, suna masu sake jinjinawa shugaba Buharin a fadar da yake yi da rashawa da cin hanci da kuma kokarin da yake yi wajen magance matsalar tsaro a kasar.

A jiya ne dai 'yan majalisun dattawa da ta wakilan na Nijeriya suka kafa wasu sharudda 12 ga shugaba Buharin da ya magance su ko kuma su dauki mataki a kansa abin da wasu suka fassara da kokarin tsige shi. Wannan matakin kuwa ya biyo bayan zargin da rundunar 'yan sandan Nijeriya take yi wa shugaba majalisar dattawa Bukola Saraki ne da hannu cikin fashi da makami da kashe-kashen da ya faru a jihar Kwara.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky