Wani Mutun Ya Yi Kokarin Kai Hari A Masallacin Madina

Wani  Mutun  Ya Yi  Kokarin  Kai Hari  A Masallacin  Madina

Wani mutum ya harba bindiga a harabar Masallacin Manzon Allah {s.a.w} da ke birnin Madinah, inda jami'an tsaron Saudiyya suka samu nasarar damke shi kafin ya kai ga aiwatar da kisan gilla.

Rahotonnin farko-farko suna nuni da cewa: Mutumin da ya yi harbe-harben dan kimanin shekaru arba'in ne a duniya, kuma yana fama da matsalar tabin hankali.

Tuni dai jami'an tsaron kasar suka yi awungaba da shi zuwa cibiyar rundunar 'yan sandan birnin Madinah domin ci gaba da gudanar da bincike kansa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky