Wani Kwale-Kwale Ya Kife A Tekun Congo

Wani Kwale-Kwale Ya Kife A Tekun Congo

Hukumomi a lardin Tshuapa dake yankin arewa maso yammacin Jamhuriyar Demokaradiyyar congo, sun ce mutum 50 ne suka rasa rayukansu bayan da wani kwale kwale ya kife a daren ranar Larabar data gabata a tekun Kongon.

Gwanan yankin Mboyo Iluka ya ce, jirgin ruwan wanda ya tashi daga kauyen Monkoto zuwa Mbandaka ya kife ne a lardin Tshuapa.

Kawo yanzu dai ba'a gano musabbabin faruwar hadarin ba.

A cewar wasu majiyoyi daga yankin, tuni aka aike da wata tawaga da ta hada da ministan harkokin ayyukan jin kai, da wasu manyan jami'ai zuwa inda lamarin ya auku domin gudanar da bincike kan wannan batu.

Sai dai a cewar hukumomi, galibi an fi danganta faruwar irin wadannan haddura na kifewar jiragen ruwa a tekun Kongo da rashin ingancin jiragen ruwan ko kuma daukar fasinjoji da suka wuce kima.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky