Wanene George Weah Zabebben Shugaban Kasar Liberia?

Wanene George Weah Zabebben Shugaban Kasar Liberia?

A ranar Alhamis da ta gabata ce 28 ga watan Disamba hukumar zaben kasar Liberia ta bada sanarwan cewa tsohon shahrerren dan kwallon kafa George Weah ne ya lashe zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a kasar.

George Weah dan shekara 51 a duniya ya lashe zaben ne da kashi 61.5% na yawan kuri'un da aka kada, inda ya kada mataimakin shugaban kasa mai ci Josept Boakai. Wannan kuma shi ne karon farko wanda za'a sauya gwamnatin kasar Liberia daga farar hula zuwa farar hula tun shekaru 70 da suka gabata.

An haifi George Weah a ranar 01 ga watan Octoban shekara ta 1966 a garin Clara kusa da birnin Liberia babban birnin kasar, shi dan kabilar Kru ne wadanda suke rayuwa a yankin kudu maso gabacin kasar, sannan daya daga cikin yankunan da suka fi fama da talauci a kasar. 

Iyayensa su ne William T. Weah da kuma Anna Quaye weah. Geoge Waeh ya fara karatu a makarantar sakandare ta Muslim Congress School sannan ya kammala a makarantar Wells Hairston High School. Kafin ya shiga harkar kwallon kafa dai ya yi aiki a matsayin kamfanin sadarwa ta kasar Liberia.

A harkar kwallon kafa kuma George Weah ya fara kwallon kafa a gida, har ma ya sami kyaututtuka masu yawa a wasannin  kwallon kafa na cikin gida. A Shekara ta 1988 Goege Weah ya fita zuwa kasashen Turai a karon farko don harkar kwallo, inda  Arsene Wenger shugaban kungiyar kwallon kafa ta Monaco ya dauke shi don wasa a cikin kungiyarsa. A lokacin da ya ke aiki da Monaco ne ya sami lamban zama zabebben dan kwallon kafa a Afrika na shekara ta 1989. Sannan a shekara ta 1991, ya ci lambar yabo ta Coupe De France, wanda ya taimakawa kungiyarsa ta Monaco kaiwa ga gasan karshe na kofin Turai ECP a shekara ta 1992.

Weah ya kulla yerjejenia da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, wacce ta dauki aro daga Kungiyar kwallon kafa ta Milan a tsakanin ta 1999-2000. Daga nan ya shiaga wasanni daban daban a wasu kungiyoyin kwallon kafa daban daban a turai, ammma kungiyar kwallon kafa ta karshe  da ya yi mata wasa ita ce Al-Jazeera ta kasar Hadaddiyar daular Larabawa, inda ya yi mata wasa har zuwa shekara ta 2003, daga nan  ya yi ban kwana da wasan kwallon kafa ya koma gida, yana dan shekara 37 a duniya. A cikin wasannin da ya yiwa kasarsa Liberia, Geoge Weah ya yi mata wasannin 60 a cikin shekaru 20 ya kuma ci mata kwallaye 22.

A lokacin da ya koma gida ya kafa kungiyar bada agaji don tallafawa mutanen kasarsa wadanda yake-yaken cikin gida ya dai-daita lamuransu. A lokacin ne Majalisar dinkin duniya ta zabe shi a matsayin Jakadan kekkyawan fafa  ko kuma " UN Goodwill Ambassador" a shekara 2004. Har'ila yau hukumar UNICEF ma ta bashi wannan matsayin. A lokacinda yake gida dai ya taimakawa matasa da dama a karatu da kuma ayyukan sana'a daga ciki har da kwallon kafa. 

A shekara 2005 ya shiga harkokin siyasa inda ya kafa jam'iyyar"The Congress for Democratic Change" ya shiga takarar shugaban kasa da Shugaban , Ellen Johnson Sirleaf. wacce ta kada shi, duk da cewa shi ne na biyu. Masana suna ganin rashin karatu mai zurfi da kuma gogewa a ayyukan gwamnatin na daga cikin dalilan faduwarsa. Amma George Weah ya sami nasarar zama Sanata a zaben ranar 20 ga watan Disamban shekara ta 2014. George Waeh yana da yayan ukku  George Weah Jr, Tita da kuma Timoty. Ya taba zama musulmi amma sai ya sake ficewa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky