Wakilan Kasashen Duniya Suna Ci Gaba Da Isa Tehran Don Halattar Taron Rantsar Da Ruhani

Wakilan Kasashen Duniya Suna Ci Gaba Da Isa Tehran Don Halattar Taron Rantsar Da Ruhani

Ya zuwa yanzu tawagogin baki daga kasashen Moldova, Britania , Portugal, Sierra Leone, Saint Thomas and Princeton, Hungary, Suriname, Guinea da kuma Lithuania, duk sun isa nan Tehran don halattar bukin rantsar da Dr Hassan Runahani a matsayin shugaban kasar Iran karo na biyu a gobe Asabar.

Ana saran wakilai daga kasashen fiye da 90 ne zasu halarciu taron rantsar da shugaba Hassan Ruhani, wanda za'a guadanar a cikin babban zauren majalisar dokokin kasar Iran a gobe  Asabar biyar ga watan Augustan shekara ta 2017. Shugaba Ruhani ne ya lashe zaben shugaban kasa karo na 12 tun bayan samun nasarar juyin juya halin musunlin ci a nan Iran. inda ya sami nasara da kuri'u miliyon 23 a zaben da aka gudanar a ranar 19 ga watan mayun wannan shekara.

Shuwagabannin da suka karaso nan Tehran dai sun hada da Ogor Dodon Shugaban kasar Moldova, Richard Bacon shugaban komitin fahintar juna tsakanin majalisun dokokin Iran da Britania. Fonseca Silva's shugaban shugaban komitin hadin guiwa na majalisun dokokin Iran da Potigal, Hassan Sharif shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin kasar Salio, GuanzillesUrbino ministan harkokin wajen kasar  São Tomé and Príncipe, Sylvester Bush Matimakin ministan harkokin wajen kasar Hungary, Anwar Mohammad wakilin shugaban kasar Suriname na musamman,  Demba Fadiga shugaban majalisar dokokin kasar Guinea, sai kuma Bros GA Darius wakilan kasar Lithuania.

A jiya Alhamis ne aka gudanar da bukin tabbatar da Dr Ruhani a matsayin shugaban kasa a gidan jagoran juyin juya halin musulunci a cikin Husainiyar Imam Khomaini ( r)288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky