Turkiyya : Abokin Takarar Erdogan Ya Amince Da Shan Kayi A Zabe

Turkiyya : Abokin Takarar Erdogan Ya Amince Da Shan Kayi A Zabe

Babban abokin hammayar Shugaba Recep Tayyip Erdogan a zaben Turkiyya, Muharrem Ince, ya amince da shan kayi a zaben shugaban kasar da aka kada a jiya Lahadi.

Mista. Ince, ya bayyana a wani taron manema labarai a birnin Ankara yau Litini cewa, ya yarda da shan kayi a zaben tare da kira ga Mista Erdogan da ya zamo shugaban dukkan al'ummarTurkawa.

Shugaba Erdogan dai ya lashe zaben ne da kusan kashi 53% na yawan kuri'un da aka kada, kamar yadda kamfanin dilancin labaren gwamnatin kasar na Anadolu ya rawaito.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky