Tsohon Shugaban Afirka Ta Kudu Na Fuskantar Shari'a

 Tsohon Shugaban Afirka Ta Kudu Na Fuskantar Shari'a

A yau Juma'a, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya gurfana a gaban babbar kotun birnin Durban saboda zargin da ake masa na cin hanci da rashawa kan wani ciniki na makamai da suka kai dala biliyan 2.5 da aka yi tun a shekarun 1990.

Ana tuhumar tsohon shugaba  Zuma, dan shekaru 75 a duniya da wasu zarge-zarge har guda 16 da suka hada da rashawa, zamba cikin aminci,  almundahana da juya kudaden haram da sauransu lamarin da a lokuta da dama ya dagula masa mulkinsa na tsawon shekaru 9, to sai dai kuma ya musanta wadannan zargin  da ake masa da cewa bai aikta wani laifi ba.

Tun da safiyar yau ne dai dubun dubatan magoya bayan Mr. Zuma din suka yi cincirindo a gaban kotun don nuna goyon bayansu a gare shi suna masu cewa akwai siyasa cikin zargin da ake masa. Zuma din ya dinga daga wa magoya bayan nasa hannu don nuna godiya ga goyon bayan da suke ba shi a lokacin da ya iso kotun.

Fara gurfanar da Mr. Zuma din a gaban kotun dai ta zo 'yan makonni bayan da ya sauka daga karagar mulkin kasar saboda matsin lambar da ya fuskanta saboda wannan zargi da ake masa. Ana ganin shari'ar dai za ta dauki lokaci ana yinta duk kuwa da wata matsalar da ta kunno kai kan ko gwamnati ce za ta ci gaba da biyan kudin dawainiyar shari'ar da ake masa din.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky