Trump Ya Gargadi Gwamnatin Syria Kan Yunkurin Kwato Idlib Daga Hannun 'Yan Ta'adda

Trump Ya Gargadi Gwamnatin Syria Kan Yunkurin Kwato Idlib Daga Hannun 'Yan Ta'adda

Shugaban kasar Amurka ya gargadi gwamnatin kasar Syria kan yunkurin da take yi tare da taimakon Rasha da Iran domin kwato yankin Idlib daga hannun 'yan ta'addan takfiriyyah masu da'awar jihadi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa, Donald Trump ya yi wannan gargadin ne 'yan kwanaki bayan da Rasha ta sanar da bankado wani shiri na yin amfani da makamai masu guba a yankin Idlib, wanda Amurka da Birtaniya da kuma Faransa suke da hannu a  cikinsa, domin dora alhakin a kan gwamnatin Syria, wanda hakan zai ba su damar samun hujjar kai mata hari, da kuma hana korar 'yan ta'adda daga Idlib.

Trump ya ce wannan yunkuri da gwamnatin Syria take na kwato yankin Idlib daga 'yan bindiga, zai iya jawo asarar rayukan fararen hula, abin da ya ce ba za su amince da shi ba.

Yankin Idlib dai shi kadai ne tya rage a hannun 'yan ta'adda a halin yanzu a kasar Syria, wanda kuma kwace iko da yankin daga hannunsu a halin yanzu, na nufin babbar nasara ce ga gwamnatin Syria, abin ko alama ba zai faranta ma Amurka da Isra'ila da wasu daga cikin kasashen larabawa rai ba


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky