TAWAQAR ‘YAN UWA ALMAJIRAN SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY SUN ZIYARCI SHEIKH ABDULJABBAR SHEIKH NASIRU KABARA Da SHEHU USMAN DAHIRU BAUC

TAWAQAR ‘YAN UWA ALMAJIRAN SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY SUN ZIYARCI SHEIKH ABDULJABBAR SHEIKH NASIRU KABARA Da SHEHU USMAN DAHIRU BAUC

Jiya talata,19 ga watan Yuni 2017 ne,wata tawaqa ta almajiran Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky karkashin jagorancin Sheikh Yakubu Yahaya Katsina suka ziyarci Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabari a mahallin da shehin malamin yake gabatar da karatun tafsirin Alkur’anin na “Jauful Fara”.
Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara malami ne masani wanda a lokaci guda kuma marubuci na kin karawa.Ya rubuta littafai masu yawa a janibobi daban daban.Sannan saboda tsabagen kauna da soyayya da shehin malamin yake nuna wa Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka,ya sanya mutane daga bangaren Salafiyya suna jifan malamin Tashayyu’I.
Sheikh AbdulJabbar ya amshi wannan tawaqa cikin girmamawa da farin ciki,sannan tawaqar ta nuna farin ciki dangane da irin tarbar da Sheikh yayi masu.
A cigaba da ziyara ta jiya,tawaqar ‘yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky karkashin jagorancin Sheikh Yakubu Yahaya Katsina suka ziyarci Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin girmama da sada zumunci.
Sheikh Dahiru Bauchi babban malamin addinin musulunci ne kuma yana daga cikin manya manyan muqaddiman Tijjaniyya a Nigeriya.Malami ne mahardacin kuma masanin tafsirin Alkur’ani da littafai,yana daga cikin wa’yanda karatukansu da maganarsu ke daukan hankalin jama’a a NIgeriya saboda hikima da iya bayani,ma’ana yana da tasiri matuka a cikin al’umman Nigeriya.
Sheikh Yakubu Yahaya Katsina yayi taqaitaccen bayani game da dalilin wannan ziyara tasu,daga cikin abubuwan da ya fadi akwai cewa:
“Dan shi’an dake zagin Sahabbai kaman dan haqiqa ne a cikin tijjaniyya ko dan izala a cikin Ahlus-Sunnah”.
A lokacin da Shehu Dahiru Bauchi yake jawabin maraba ga wannan tawaqa ya shaida cewa:
“Duk musulmi shi’ar Annabi Muhammadu ne,idan musulmi yace baya shi’a sai mu kore shi.Mun sha yin wazifa tare da Sheikh Zakzaky,sannan gashi kun yi sallah a bayana na kuma kun yi salatul Fatihi.
“Maganar zagin Sahabbai kuwa tattaunawa da masu hankali cikinku yasa mun fahimci ‘yan haqiqan dake cikinku sune suke yi.Don haka mun yarda da abubuwanku dari bisa dari kaman yadda kuka yarda da na mu.
Wannan tawaqa ta Sheikh Yakubu Yahaya tayi sallah tare da Shaikh Dahiru,sannan suka yi buda baki tare da shi a masaukinsa dake Kano.

Ziyara

Ziyara

Ziyara

Ziyara

Ziyara

Ziyara

Ziyara

Ziyara

Ziyara

Ziyara


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky