Taron Shugabanin Kungiyar ECOWAS Na Gudana A Kasar Ghana

Taron Shugabanin Kungiyar ECOWAS Na Gudana  A Kasar Ghana

Shugabanin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO sun fara gudanar da taronsu karo na biyar da nufin lalubo hanya mai sauki na samar da kudin bai daya a tsakanin kasashen.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya habarta cewa a jiya laraba shugabanin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka sun fara gudanar da taronsu karo na biyar da nufin samar da hanya mafi sauki na samar da kudin bai daya a tsakanin kasashen a birnin Acrra fadar milkin kasar Ghana.

Kafin haka dai, kwamitin kungiyar ta ECOWAS ya sanar da cewa cimma wannan manufa zai matukar wahala saboda yanayin kudaden wasu kasashen da suke da karfi a cikin kungiyar musaman ma Najeriya da Ghana.

Tun a shekarar 2000 ce, kungiyar ta samar da wannan tunani, inda take sa ran a shekarar 2020, za ta samar da kudin bai daya da za a dinga amfani da shi a kasashen dake cikin kungiyar.

Yankin yammacin Afirka na da kasashen 15, takwas daga cikin su na amfani da kudin CFA,sannan sauren bakwai din ko wanne na da nasa kudin da yake amfani da shi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky