TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARAI

TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARAI

MUNA ALLAH WADAI DA HARIN DA ‘YAN SANDA SUKA KAI KAN ZAMAN DIRSHAN DIN MU A ABUJA

Gamayyar jami’an tsaro ‘yan Sanda, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan Sanda na babban birnin tarayya Abuja, dauke da muggan makamai, kulake, motar sulke, tankar ruwan zafi da karnuka, da ma wadansu ‘yan Sandan a bisa dawakai, a ranar Juma’a 13/04/2018, suka zagaye Dandalin ‘yanci (Unity Fountain) da ke garin Abuja da nufin kawo karshen zaman-dirshan na fafutukar ganin an saki Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda gamayyar kungiyoyi bisa jagorancin Concern Nigerians suke gudanarwa.

Jami’an tsaron ‘yan Sanda sun yi amfani da Barkonon tsohuwa domin tarwatsa jama’a, kuma Kwamishinan ‘yan Sanda ya kama Mukaddamin zaman dirshan din, Prince Deji Adeyanju ya tsare shi tsawon sa’o’i haka-siddan kuma ba tare da an tuhume shi da aikata wani laifi ba.

Irin wannan muzgunawa da harzukawa daga manyan jami’an tsaro rashin sanin makamar aiki ne tare kuma da tauye mana ‘yancin mu na gudanar da taro da kuma gudanar da Muzahara ta lumana.

Muna yin Allah wadai da babbar murya dangane da wannan lamari. Tsawon kwanaki tamanin da biyar da fara gudanar da wannan Zaman Dirshan da kuma tsawon lokacin da aka dauka ana gudanar da fafutukar ganin an saki Shaikh Zakzaky, masu gudanar da Muzaharorin suna aiwatar da lamuransu cikin tsari da lumana. Duk kuwa da irin hare-hare na ta’addanci da jami’an tsaro suke kaddamarwa a kan masu gudanar da Muzaharorin, ba mu taba yin amfani da hanya ta tashin hankali ba wajen cimma manufofinmu.

Irin wannan aiki na rashin kan-gado da kuma saba wa doka ba zai kawo karshen fafutukar ganin bayan zalunci da yi wa doka karan-tsaye ba da kuma tabbatar da adalci. Haka nan kuma ba zai hana fafutukar ganin an bi umarnin kotu ba na Sakin Shaikh Zakzaky ko kuma kiraye-kiraye na a kama tare da hukunta wadanda suka kaddamar  da aika-aikar kisan kiyashin Zariya a cikin watan Disambar 2015 ba.

Muna so mu yi amfani da wannan dama wajen wayar da kai da kuma shelanta wa daukacin al’umma cewa su yi watsi da bayanai na karya da kuma Farfaganda wadda Jami’an tsaro suke yadawa na cewa tarukanmu a garin Abuja na fafutukar ganin an Saki Shaikh Zakzaky lamari ne na barazana ga sha’anin tsaro. Jagoranmu bai taba aikata aiki na tashin hankali ba, bilhasali ma gidansa ya kasance wurin aminci ga Kiristoci da kuma raunanan jama’a marasa karfi da rinjaye a yayin fadace-fadace da aka yi a lokutan da suka gabata. Don haka fadi-tashin ganin an saki`Shaikh Zakzaky ba zai taba zama mai barazana ga mutanen da ake nuna musu danniya ba. Idan yau ana zaluntar Shaikh Zakzaky, wa ya san kuma gobe wa za a zalunta?

Don haka, muna kira ga dukkanin kungiyoyi da su hada hannu da mu wajen wannan fafutuka tamu ta lumana ta ganin bayan zalunci da azzalumai da raina umurnin kotu. Haka nan kuma muna rokon dukkanin ‘yan Najeriya, Kungiyoyi  da kuma jama’a ma’abota hankali da adalci da su yi kira ga mahukunta, musamman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da ya saki Shaikh Zakzaky, mai dakinsa, Malama Zeenatuddeen, da kuma sauran ‘yan uwan mu da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba a wuraren tsare jama’a mabambanta da ke fadin tarayyar Najeriya kamar yadda babbar kotu a tarayyar Najeriya ta bayar da umarni.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA
Skype:Ibrahim.musa42
14/04/2018


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky