Ta'addancin Somaliya Ya Hallaka Rayuka Da Dama

Ta'addancin Somaliya Ya Hallaka  Rayuka  Da Dama

Akalla mutane 20 suka mutu yayinda da wasu sama da 40 suka jikkata bayan tashin wasu bama-bamai da aka sanya cikin motoci a birnin Mogadisho na kasar Somaliya, yau juma’a.

Kakakin 'yan sandan kasar ta Somaliya Ali Nur ya ce; An kai harin ne a kusa da ginin hukumar 'yan sanda ta binciken manyan laifuka.

 Bugu da kari kakakin 'yan sandan ya ci gaba da cewa; galibin mutanen da suka rasa rayukan nasu a harin na jiya juma'a fararen hula ne sai kuma tsirarun jami’an tsaro da ke kan hanya.

Kakakin 'yan sandar ya ce 'yan kunar bakin wake sun kai harin ne a wani otel da ke kusa da hedkwatar sashen binciken manyan laifuka na 'yan sanda kasar (CID).

Tuni kungiyar ta'addancin nan ta ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alqa'ida ta dauki alhakin kai harin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky