Sojojin Sudan Sun Fara Ficewa Daga Yamen

Sojojin Sudan Sun Fara Ficewa Daga Yamen

Wasu daga cikin sojojin Sudan da suke yaki karkashin rundunar kawancen Saudiyya a kasar Yamen sun fara komawa gida sakamakon matsin lamba da suke fuskanta.

Tashar Arabiyya 21 ta watsa rahoton cewa: Wata bataliyar sojin Sudan da aka aike zuwa kasar Yamen, bayan shafe watanni takwas a karkashin rundunar kawancen Saudiyya a yankin arewa maso yammacin kasar Yamen ta dauki matakin komawa Sudan.

Wasu rahotonni suna bayyana cewa: Janye bataliyar sojin ta Sudan daga kasar ta Yamen ya zo ne bayan matsin lamba da gwamnatin kasar take ci gaba da fuskanta daga al'ummar Sudan musamman ganin yadda ake yawaita kashe sojojin Sudan a yankin arewa maso yammacin kasar ta Yamen.  


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky