Sojojin Siriya Sun Kwace Al-Boukamal, Birnin Karshe A Hannun IS

Sojojin Siriya Sun Kwace Al-Boukamal, Birnin Karshe A Hannun IS

Rundinar sojin Siriya ta yi nasara kwace Al-Boukamal, birnin na karshe da ke hannun 'yan ta'adda na IS gabashin kasar.

Birnin Al-Boukamal shi ne wani sansani na karshe inda sauren 'yan ta'addan na IS suka buya bayan fatatakarsu daga yankin Deir Ezzor na Siriya da kuma birnin Al-Qaïm na Iraki.

Baynai sun nuna cewa an murkushe 'yan ta'addan a cikin gajeren lokaci, ba kamar yadda akayi tsammani ba tun da farko cewa yakin zai yi tsanani, duk da cewa dai dakarun Rasha hadin gwiwa da na Siriya sun yi amfani da mayan dabaraun yaki.

Ko baya ga hakan bangarorin sun samu dauki daga mayakan kungiyar Hezbollah na Labanon, sannan daga wani bangaren sun samu dauki daga mayakan sa kai na 'yan shi'a a iyaka da Iraki.

Kwace birnin Al-Boukamal, ya sanya a yanzu kungiyar IS ba ta rike da gari ko guda a Iraki da Siriya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky