Sojojin Nijeriya Sun Sanar Da Raunana Wani Daya Daga Cikin Shugabannin Boko Haram

 Sojojin Nijeriya Sun Sanar Da Raunana  Wani Daya Daga Cikin Shugabannin Boko Haram

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewar dakarunta sun sami nasarar raunana shugaban daya daga cikin bangarorin kungiyar nan ta Boko Haram ta kasar Mamman Nur, rauni mai tsanani.

Rundunar sojin ta Nijeriya ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce an wani hari da sojojin Nijeriyan suka kai wani waje da ake zaton nan ce helkwatarsa, sojojin sun sami nasarar raunana Mamman Nur din wanda ya balle daga asalin kungiyar ta Boko Haram karkashin jagorancin Abubakar Shekau a baya.

Kakakin harin nan ta Operation Lafiya Dole, Onyema Nwachukwu ya ce an raunana Mr. Nur din ne sakamakon ruwan bama-baman da sojojin Nijeriyan suka yi a tungar 'yan Boko Haram din inda aka raunana shi rauni mai tsanani sai dai kakakin bai yi karin bayani kan wajen da aka kai harin da kuma yadda suka samu tabbacin cewa an raunana Mamman Nur din ba.

Har ila yau Kakakin ya ce baya ga shugaban Boko Haram din har ila yau kuma an kashe wasu daga cikin dakarun kungiyar sannan wasu kuma suna ta mika kansu ga sojojin Nijar


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky