Sojojin Hayar Saudiya 4 Ne Suka Hallaka A Yemen

Sojojin Hayar Saudiya 4 Ne Suka Hallaka A Yemen

Majiyar tsaron kasar Yemen ta sanar da hallaka sojoji 4 na bangaren tsohon Shugaban kasar da ya yi murabus Abdu Rabahu Mansoor Hadi a jihar Ma'ari

Majiyar ta kara cewa baya ga sojojin da aka kashe, an kame wasu 4 na daban a yankin Saraawih na jihar Ma'arib.

A cikin kwanakin biyu da suka gabata, Sojoji da dakarun sa kai na kasar Yemen din sun samu nasarar hallaka ko jikkata sojojin hayar Saudiya 23 a fagen daga na jahohin Ta'iz da Aljauf.

Har ila yau a ranakun Juma'a da Asabar da Lahadi da suka gabata, Sojoji da dakarun sa kai na kungiyar Ansarullah sun samu nasarar hallaka sojojin hayar Saudiya 22 a  kasar ta Yemen.

Tun a watan Maris din 2015 ne kasar Saudiya bisa goyon bayan Amurka ta fara kai hare-hare kan al'ummar kasar Yemen tare da killace kasar ta sama, kasa da kuma ruwa, inda ya zuwa harin yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba wasu milyoyin da mahalinsu.

A matsayin mayar da martani, sojoji da kuma dakarun sa kai na kasar ta Yemen na harba rokoki kan matattarar sojojin hayar Saudiya a cikin kasar da kuma cikin kasar ta Saudiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky