Siyasar Amurka Ta Kin Jinin Iran Ba Za Ta Je Ko'ina Ba

Siyasar Amurka Ta Kin Jinin Iran Ba Za Ta Je Ko'ina Ba

Mai ba da shawara ga shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ne ya bayyana haka a lokacin da yake ishara da takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran

Husain Amir Abdullahiyan ya ci gaba da cewa; Tun daga cin nasarar juyin musulunci zuwa yanzu, duk wani abu da Amurka za ta iya yi na kiyayya, ta yi shi akan Iran,amma kuma babu inda ya kai ta.

Amir Abdullahiyan wanda tashar talabijin din Russia Today ta yi hira da shi, a jiya juma'a, ya ci gaba da cewa; Shugaban kasar Amurka Donald trump yana son shelanta wani yaki ne na bayan fage akan Iran ta fakewa da kakaba takunkumi.

Dangane da zargin da Saudiyya take yi wa Iran na bai wa sojojin Yemen makamai, Abdullahiyan ya yi watsi da zargin yana mai cewa; Kasar Yemen da dade da mallakar makamai tun zamanin Ali Abdllah Saleh.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky