Siriya :Akwai Yi Yuwar Barkewar Wani Sabon Yaki

Siriya :Akwai Yi Yuwar Barkewar Wani Sabon Yaki

Shugaba Bashar al-Assad, na Siriya, ya yi barazanar yin amfani da karfi kan mayakan Kurdawa dana Larabawa dake samun goyan bayan Amurka.

Mista Assad wanda ke bayyana hakan a wata hira da tashr talabijin ta Russia Today, ya ce zamu iya yin amfani da karfi don kwato yankunan dake karkashin mayakan a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaba Assad ya kuma ce a shirye yake ya tattauna da mayakan na FDS, amma idan hakan ya cutura, to zamu tsarkake yankunan da karfi.

A hannu daya kuma shugaban Siriyar ya ce, saura kiris a fafata tsakanin tsakanin dakarun Amurka dana Rasha a kasarsa, saidai an sa'ar kauce wa hakan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky