Shugaban Mohammad Yusuf Na Jumhuriyar Nijar Ya Ziyarci Shugaba Buhari Na Najeriya A Daura

Shugaban Mohammad Yusuf Na Jumhuriyar Nijar Ya Ziyarci Shugaba Buhari Na Najeriya A Daura

Shugaban jamhuriyar Nijar Mohammad Yusuf ya ziyarci takwaransa na tarayyar Najeriya wanda yake hutun salla a garinsu Daura a jiya Talata

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa shugaban Nijar ya sauka a tashar jiragen sama na Ummaru Musa Yar'aduwa dake Katsina inda bayan karban fareti tare da gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari shuwagabannin biyu suka hau jirgi mai saukar ungulu zuwa Daura..

Shugaba Yusuf ya bayyana cewa ya zo Daura ne don gaida shugaba Buhari dangane da rashin lafiyan da yayi ta fama da shi da kuma ya masa addu'ar karin lafiya. 

Har'ila yau kara da cewa a ganawarsa da shugaba Buhari sun tattauna batun tsaro na kan iyakokin kasashen biyu da kuma matsalolin tafkin shadi. Daga karshe ya ce sun yi maganar dangantakar kasashen biyu.

A nasa bangaren shi ma shugaba Buhari ya godewa shugaba Yusuf da ziyarar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky