Shugaba Muhammadu Buhari Yayi Kira Ga 'Yan Nigeriya Dasu Rungumi Zaman Lafiya

Shugaba Muhammadu Buhari Yayi Kira Ga 'Yan Nigeriya Dasu Rungumi Zaman Lafiya

A cikin sakon shugaba Muhammadu Buhari na taya musulmi murnar sallah babba yayi kira ga 'yan Nigeriya da su rungumi zaman lafiya,yana cewa:

"A irin wannan lokaci na farin ciki na wannan shekarar wanda muke yin bukin sallah babba,ina rokon dukkan 'yan Nigeriya da su tashi su kawar da bambamce bambamce,mu ajiye son zuciyar mu a gefe guda,kana mu karfafi abota da hadin kai domin kasar mu ta cigaba da kasancewa a hade."
Shugaba Buhari ya cigaba da cewa:
''wajibi ne 'yan Nigeriya su koyawa kawukansu ganin cewa dukkansu 'yan uwan juna ne maza da mata wadanda suke da tarihi da gado daya ....'
Sannan Buhari ya taya dukkan musulmin Nigeriya da duniya baki daya murnar salla babba ta wannan shekarar.Sannan ya taya wadanda suka samu daman zuwa kasar Makkah domin sauke farali murna.
A karshe Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna jin dadinsa da godiya game da yanda 'yan Nigeriya suka dinga yi masa addu'a akan Allah ya bashi lafiya a lokacin da ya tafi jinya kasar Ingila.Yace wannan ya kara masa karfi da himma akan dole ne ya sadaukar da kanshi wajen gina Nigeriya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky