Shugaba Hassan Rauhani: Iran Za Ta Bunkasa Alakarta Da Kasar Zimbabwe

Shugaba Hassan Rauhani: Iran Za Ta Bunkasa Alakarta Da Kasar Zimbabwe

Shugaban na kasar Iran da ya gana da takwaransa na kasar Zimbabwe Robert Mogabe, ya ce; Kasashen biyu suna da dama mai yawa da su iya bunkasa alakarsu a cikinsu.

Shugaba Hassan Rauhani ya ci gaba da cewa; Fagagen da kasashen biyu za su iya aiki akansu sun hada da noma, ilimi, al'adu da masana'antu.

Rauhani ya ci gaba da cewa al'ummar Zimbabwe, al'umma ce mai gwagwarmaya, kuma tamkar al'ummar Iran suna cin gashin kansu da 'yanci, don haka su ke da alaka da juna tun farkon cin nasarar juyin musulunci.

Robert Mubage dai ya iso Iran ne domin halartar bikin rantsar da shugaban Hassan Rauhani a zango na biyu na mulkinsa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky