Shugaba Buhari Ya Shelanta Niyarsa Ta Sake Tsayawa Takarar Shugabancin Kasa

Shugaba Buhari Ya Shelanta Niyarsa Ta Sake Tsayawa Takarar Shugabancin Kasa

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto cewa a jiya Laraba shugaba Muhammadu Buhari dan shekaru 75 ya ziyarci ofishin jam'iyyar APC mai mulki inda ya cike fom din tsayawa takara

Muhammadu Buhari wanda tsohon shugaban kasar na soja ne, an zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2015 wanda a karon farko ya yi nasara akan shugaban da ke kan karagar mulki Goodluck Jonathan.

shugaba Buhari ya yi alkawalin fada da cin hanci da rashawa a cikin kasar da take da tattalin arziki mafi girma a nahiyar Afirka.

Sake tsayawa takarar da shugaba Buhari ya yi, ya zo ne a lokacin da kasar take fama da matsalolin tsaro wanda yake tasiri ga bunkasar tattalin arzikin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky