Shugaba Buhari Ya Sake Komawa London Domin Kula Da Lafiyarsa

Shugaba Buhari Ya Sake Komawa London Domin Kula Da Lafiyarsa

Shugaba Buhari na tarayyar Najeriya ya sake tafiya birnin London na kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.

Mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa shugaba Buhari ya sake tafiya London ne domin ya ga likitocinsa a kan rashin lafiyarsa, kuma a cewarsa babu wani abin damuwa dangane yanayin nasa.

Adesin bai yi karin haske a kan lokacin da shugaba Buhari zai dawo Najeriya ba, amma dai ya tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar Farfesa Osinbajo ne zai ci gaba da mulkin kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa, kuma tuni Buhari ya aike wa majalisar dattijai da wasika da ke sanar da su hakan.

Shugaba Buhari dai ya dauki tsawon kwanaki ba a gan shi ba, lamarin da ya jawo magnganu masu karo da juna a tsakanin 'yan kasa, amma a ranar Juma'a da ta gabata shugaban ya halarci sallar Juma'a a cikin masalalcin da ke fadarsa, bayan kammmala sallar kuma ya koma cikin gida, a jiya kuma ya gana da 'yan matan Chibok 82 da aka yi musayarsu da mayakan Boko Haram.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky